Pillay ta girgiza da abinda ta gani a CAR

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Navi Pillay

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da wani mummunan bayani game da rikicin kwanan baya a Jamhuriyar tsakiyar Afrika, bayan wata ziyarar kwanaki uku a kasar.

Navi Pillay ta ce an yi wa yara gunduwa-gundawa kuma makasan sun rinka cin naman wadanda suke kashewa.

Ta kara da cewar kiyayya tsakanin al'umma ta kai wani matsayi na inna-niha, kuma ana azabtar da mutane, tare da daddatsa su, da kuma konawa.

Sai dai ta ce tura dakarun Faransa da na Afrika ya dakatar da dinbin kisan mutanen ya zuwa yanzu.

Karin bayani