An rufe dandalin Twitter a Turkiyya

Image caption Mr Erdogan ya ce bai damu da duk wani martani da zai biyo baya ba daga kasashen duniya.

Rahotanni daga Turkiyya na cewa ana rurrufe hanyoyin shiga shafin sadarwa na intanet na Twitter, sakamakon barazanar da firai ministan kasar Recep Tayyip Erdogan, yayi ta rufe dandalin.

Masu amfani da shafin da suka yi kokarin shiga sun ce, ana nuna musu wata sanarwa ta kamfanin kula da harkokin sadarwa na Turkiyyan da ke cewa an rufe dandalin sabo da wani umarni na kotu.

Tun da farko dai Mr Erdogan, wanda ke cikin wata babbar badakala ta almundahana, ya sheda wa dubban magoya bayansa , a yayin wani gangamin yakin neman zabe cewa zai kawar da dandalin na Twitter.