Sojojin Nigeria sun gano makamai a Borno

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamaru za ta bada sojoji domin tabbatar da tsaro a tafkin Chadi

Dakarun Najeriya sun ce sun gano wasu jibgin makamai da aka binne a wani cocin da aka kona, a karamar hukumar Kalabalge dake Jihar Borno.

A wata sanarwar da rundunar ta fitar dake dauke da sa hannun kakakinta, manjo janar Olukolade sojin sun ce, makaman sun hada da bindiga mai harbo jiragen sama da bindiga mai sarrafa kanta da dubban alburusai.

Sanarwar ta ce wani dan ta'adda da ya yi ikirarin cewa dan Kamaru ne, shi ya kai su maboyar makaman da aka adana, domin kai hare-hare a garuruwan da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru.

Rundunar ta kara da cewa an kwashe dukkan makaman, kuma sojoji na cigaba da sunturi, domin tabbatar da tsaro a yankin da kewayensa.