An tsare likita a saboda yi wa mace kaciya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yanzu haka mutane biyu na tsare kan batun

A karon farko gwamnatin Birtaniya ta bada sanarwar gurfanar da wasu mutane 2 a gaban shari'a bisa zargin yi wa mata kaciya.

Ana zargin likita Dhanoun Dharmasena ne da laifi yi wa wata mata kaciya, bayan ta haifu a wani asibiti dake nan London.

Shi kuwa mutumen na biyu, Hassan Mohammed, ana zarginsa ne da karfafa wa Dr Dharmasena gwiwa .

Su ne dai mutane na farko da suka gurfana a gaban shari'a, duk da cewa an kafa dokokin dake haramta kaciyar mata a Birtaniya tun shekarar 1985.

Wakiliyar BBC ta ce a baya ana cewa Birtaniya ba ta yi dgaske a fannin yaki da kaciyar mata, idan kwatanta ta da Faransa inda aka hukunta mutane fiye da 100 da suka aikata irin wannan dabi'a.

Karin bayani