An yi wa dokar aure kwaskwarima a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta

Majalisar dokokin Kenya ta amince da wani kudurin doka a kan aure, wanda zai baiwa maza auren mata iya san ransu, ba tare da sun shaidawa uwargidansu ba.

'Yan majalisar dokoki mata sun fice daga zauren majalisar bisa adawa da wannan sabon kudurin.

Dokar ta baya da aka yi wa kwaskwarima, ta baiwa maza damar auren mace fiye da daya amma kuma sai mazan sun shaidawa uwargidansu.

Sabuwar dokar ta ce dole ne mutum ya yi rijistar aurensa, sannan mace sai ta kai shekaru 18 kafin a aurar da ita.

Sannan majalisar ba ta amince da batun raba dukiya daidai tsakanin mace da namiji idan auren ya mutu.

Karin bayani