'Yan adawa a Algeria zasu kauracewa zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa sun ce Bouteflika ba shi da kosashiyar lafiya

Dubunnan 'yan adawa a Algeria sun gudanar da zanga-zanga a Algiers, babban birnin kasar domin neman a kauracewa zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan gobe.

Jam'iyyun adawa - masu kishin Islama da wanda babu ruwansu da addini - ba su amince da yunkurin Shugaba Abudul'azeez Bouteflika na neman kara darewa kujerar mulki a karo na hudu ba.

Sun ce wani bugun jini da ya samu a bara, ya sa ba zai iya ci gaba da shugabanci ba.

An dai kwashe watanni, Mr Bouteflika mai shekaru saba'in da bakwai bai bayyana a fili ba.