Masar: An soma shari'ar magoya bayan Morsi

Hakkin mallakar hoto Getty

Fiye da magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi, su dari biyar ne suka gurfana a gaban alkali É—azu a Birnin Alkahira.

Dukkan mutanen dai 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ne.

Ana zargin su ne da tunzura jama'a don su tada hankali da kuma kasancewa 'yan ta'adda.

Shari'ar tasu dai ita ce mafi girma a kasar.

Wasu karin mutane 700 ne kuma ake saran zasu gurfana a gaban alkali ranar Talata mai zuwa.