Guinea: Kwayar cutar Ebola ta kashe mutane 60

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar mai saurin yaduwa ta bulla ne makonni shida da suka wuce.

Masana kimiyya a Faransa sun ce kwayar cutar Ebola ce sanadiyyar annobar da ta barke a kasar Guinea, wacce ta kashe kusan mutane sittin.

Cutar mai saurin yaduwa ta bulla ne makonni shida da suka wuce.

Alamunta sun hada da zubar jini, tare da amai da gudawa.

Wani jami'in ma'aikatar lafiya ta kasar Guinea ya ce kimanin mutane tamanin ne suka kamu da cutar, mafi yawansu a kudancin kasar.