Ivory Coast ta mika Ble Gaude ga ICC

Ofishin ICC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ofishin ICC

Ivory Coast ta mika Charles Ble Gaude, wani tsohon shugaban mayakan sa kan kasar ga kotun muhunta manyan laifuka ta ICC dake Hague.

Ana zargin Ble Gaude, wanda na kusa ne ga tsohon shugana kasar, Laurent Gbabgo, da rura wutar rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar a 2010.

Can dama dai kotun na neman sa don amsa tuhumar da ake yi masa.

Yanzu haka tsohon shugaban Ivory Coast din wato Laurent Gbagbo na zaman jiran shara'a a gaban kotun