Fafaroma ya kafa kwamiti akan lalata da yara

Fafaroma Francis ya nada wani kwamitin da zai rika ba shi shawara akan yadda za a shawo kan matsalar bata yara da ta addabi cocin roman katolika a 'yan shekarun nan.

Kwamitin mai mambobi 8, ya hada da wata 'yar Ireland mai suna Marie Collins wadda ita ma wani limamin coci ya taba cin zarafinta.

Wakilin BBC yace an soki lamirin Fafaroman da saboda jan kafar da ya ke yi akan matsalar bata yaran da ta zubawar da kimar cocin roman katolika.

Amma wani mai magana da yawunafaroman yace fafaroman yanzu ya dage wajen ganin an shawo kan matsalar