Somalia:Dakarun Afirka sun tunkari Koryoley

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kama birnin Koryolev zai kasance nasarar rundunar mafi muhimmanci a watan da ake ciki

Darurunwan dakarun Tarayyar Afirka a Somalia sun dumfari muhimmin birnin Koryoley, mai nisan kilomita casa'in kudu maso yammacin Mogadishu, babban birnin kasar.

Birnin Koryoley na karkashin ikon kungiyar masu kishin Islama ta Al-Shabab ne tun shekaru biyar da suka wuce.

Wakilin BBC a yankin ya ce kama birnin, zai kasance nasarar rundunar mafi muhimmanci tun farkon fara kai farmaki kan mayakan Al-Shabab a cikin watan nan.

Ash-Shabab, mai alaka da al-Qaeda ta kwashe shekaru takwas ta na gudanar da yaki da nufin kifar da gwamnatin Somali mai samun goyon bayan Majalisar dinkin duniya tare da kafa gwamnatin Musulunci.