Za a tura jami'an sa ido zuwa Ukraine

Image caption Masu sa idanun ba zasu je Crimea ba

Hukumar tsaro ta nahiyar Turai, OSCE, wacce ta kunshi Rasha da Tarayyar Turai, ta amince da tura jami'an sa ido na kasa da kasa zuwa Ukraine.

Da fari dai za'a tura jami'ai dari ne zuwa sassan kasar, ciki kuwa har da yankunan 'yan kabilar Rasha dake gabashin Ukraine, amma ban da Crimea.

Jakadan Amurka a hukumar tsaron turan, Daniel Baer ya ce kasarsa na maraba da amincewar da Rasha ta yi da batun tura masu sa idon.

Sai dai wakilin Rasha a hukumar ya ce masu sa idanun basu da hurumin zuwa yankin Crimea.