Boko Haram: Mata sun shiga halin ni 'yasu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan boko haram sun kashe akalla mutane hamsin a gaban wata yarinya

BBC ta samu bayanin tashin hankalin da wasu 'yan mata suka gani, lokacin da 'yan kungiyar da wasu ke kira Boko Haram suka kama su a Nigeria.

Wata budurwa mai shekaru23 ta shaida wa BBC cewa, mayakan Boko Haram sun kashe akalla fararen hula 50 a gabanta, a wani sansaninsu da ke arewa- maso-gabashin kasar.

Ta ce mafi yawan wadanda aka kashe, yankasu aka yi.

Daya budurwar kuma ta ce mayakan kungiyar sun nemi su tilasta mata ta kashe wadanda aka kama su tare.

'Yan matan dai sun samu tsere wa daga hannun 'yan kungiyar, inda yanzu kuma suke rayuwa a boye.