Nigeria: 'Yan sanda sun gano gawarwaki

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sanda a Nijeriya sun ce, sun gano gawarwaki da suka soma rubewa da kokon kan mutane da sauran sassan mutane a wani gida da ba a amfani da shi a Ibadan.

An kuma gano mutane goma sha biyar cikin mari da kuma wasu mutanen da suka yi matukar ramewa a kusa da wurin.

Tuni dai aka kama wasu dake da alaka da lamarin, amma ba kai ga kama mutumin da ke da wuraren ba.

An dai gano wannan wuri ne bayan wasu 'yan achaba sun yi korafin cewa, abokan aikinsu da dama suna salwanta.