NLC ta koka akan 'ɓarna' a gwamnati

Image caption Ana samu karuwar masu amfani da jiragen sama a Nigeria

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ta fitar da sanarwa yau tana kokawa akan abinda ta kira karuwar barna da dukiyar jama'a da ake aikatawa a dukkan matakan gwamnati.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau dauke da sa hannun shugabanta, Abdulwaheed Omar ta ce, abin takaici ne yadda manyan jami'an gwamnati suke kashe kudade masu yawa wajen amfani da jiragen sama na ƙasaita.

NLC ta ce, manyan jami'an gwamnatin suna kashe mukuden kudaden ne duk da cewar, kasar tana fama da rashin aikin yi da karancin ababan more rayuwa.

Babbar kungiyar kwadagon ta kuma zargi gwamnoni da ministoci da barnata kudade wajen amfani da jiragen saman na alfarma, amma kuma suna korafi cewa babu kudi.

Kungiyar NLC ta kuma bayyana takaici akan zargin barnata naira miliyan 130 da ministar man petur, Diezani Allison Madueke take yi kowanne wata a hayar jirgin sama.

Ta kuma yabawa majalisar wakilai saboda yunkurin yin bincike akan wannan batu.