Yaduwar cutar Ebola a Guinea

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an kiwon lafiya sun bazama a Conakry

Jami'an lafiya a Guinea sun ce gwajin da aka yi a kan mutane biyu wadanda aka yi zaton sun rasu ne a sakamakon kamuwa da kwayar cutar Ebola a Conakry babban birnin kasar, bincike ya tabbatar da cewa basu kamu da kwayar cutar ba.

Masana kimiyya a cibiyar Pasteur a Senegal suna ci gaba da kokarin gano ko wane irin nau'in kwayar cutar ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.

A ranar Lahadi Majalisar Dinkin Duniya ta ce kwayar cutar Ebola wadda ta hallaka mutane kusan sittin a kudancin Guinea ta yadu zuwa babban birnin kasar.

Wata mai magana da yawun kungiyar likitoci ta Medicines San Frontiers, Gemma Dominguez ta ce annobar ta tsoratar da jama'a a babban birnin kasar ta Guinea

Tace "Matsalar ita ce abin da ke faruwa yanzu a Conakry hankula sun tashi sannan ga firgici. Ba abu ne mai sauki ba saboda cuta ce mai hadari."

Karin bayani