An yi zanga-zanga a Ibadan game da wani gida

taswirar Najeriya
Image caption taswirar Najeriya

A Najeriya tarzoma ta barke a gaban wani kangon gini a kudu maso yammacin kasar, inda a ranar Asabar da ta wuce aka gano rubabbun gawarwakin mutane, da kuma wasu dauraru.

Masu zanga zangar sun far ma wurin ne da kusa da birnin Badun, da niyyar gano wasu 'yan uwansu da suke zargin sun bata.

Ana zargin dai ana amfani da wurin ne don tsaubbace-tsubbace ko kuma sayar da sassan jikin dan Adam.