Hukuncin kisa kan magoya bayan Morsi 529

Magoya bayan Muhammad Morsi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Talata ne za a fara shari'ar wasu magoya bayan Morsi su 700

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin kisa ga mutane 529, ciki har da shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi.

Hukuncin ya shafi Magoya bayan Muhammad Morsi 150 da ke tsare, da sauran da aka yanke wa hukunci a bayansu, sai wasu mutane 16 da kotu ta wanke.

An sami mutanen 529 da hannu a laifin kisan wani dan sanda tare da far wa 'yan sanda, a lokacin zaman durshen nuna goyon baya ga hambararren shugaban.

Jami'an tsaro sun tarwatsa zaman durshen din da aka yi, a watan Agustan shekarar 2013 da karfin tuwo.

Lauyoyin da ke kare mutanen sun ce, ba a basu damar kare wadanda aka samu da laifin sosai ba, kuma ana sa ran za su daukaka kara.