G7: Obama ya isa Netherlands

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama ya ce Rasha za ta gane kurenta

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa kasar Netherlands inda zai hadu da sauran shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya G7 kan matakin da za su dauka a kan Rasha sakamakon shigar da yankin Crimea da ta yi a cikin kasarta.

Obama ya ce kasashen Turai da Amurka kan su a hade yake wajen taimakawa gwamnatin Ukraine da jama'arta.

Kana yace tattalin arzikin Rasha zai raunana sakamakon abin da ta aikata.

A waje daya kuma, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a karon farko tun bayan da Amurka ta sanyawa Moscow takunkumin tattalin arziki.

Karin bayani