Yara miliyan na kamu wa da tarin TB

Hakkin mallakar hoto Carlos Cazalis
Image caption Tarin fuka cuta ce mai yaduwa ta iska, saboda haka ana daukarta

Wani sabon bincike na nuna cewa ana samun yara kimanin miliyan daya dake kamuwa da cutar tarin fuka duk shekara a duniya.

Hakan dai ya ninka adadin da ake tunani a baya, a cewar binciken da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta Lancet, da ya zo daidai da ranar tarin fuka na duniya (24th March).

Binciken ya gano cewa yara da dama suna mutuwa ba gaira babu dalili, saboda kashi daya cikin uku na cutar kawai ake gano wa.

Masu binciken sun ce cutar na saurin kama yara, saboda haka ana bukatar kayayyakin gwaji masu inganci, domin samun kulawar da ta dace.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin mutane miliyan 1.3 ne suka mutu a sanadiyyar tarin TB, a shekarar 2012.

Dr. Gidado Mustapha kwararren likita ne kan cutar tarin fuka a Najeriya, ya kuma bayyana hanyoyin kariya daga kamuwa daga cutar kamar haka:

  • A tafi asibiti da zarar kamu wa da cutar, domin shan magani
  • Wanda ke tari fiye da makonni biyu ya je asibiti, domin yin gwaji kyauta
  • Ka da mai cutar ya dinga kaki yana zubar wa a kasa
  • Idan mai cutar na cikin jama'a, a dinga bude tagogi
  • Kada a stangwami mai cutar, domin tana warke wa
Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Kwayar cutar tarin fuka ko TB

Dr. Gidado ya ce akwai masu fama da cutar kimanin dubu 134 a Najeriya, a shekarar 2012, yayin da a shekarar 2002 ake da masu fama da tarin fuka dubu 11 kawai a kasar.

Likitan ya danganta karuwar masu cutar da yawan asibitoci dake bada kulawa da aka samu, inda ake da asibitoci 5000 dake bada magunguna a fadin kasar.

Haka kuma an samu karin dakunan gwajin cutar daga 500 zuwa 1, 500 a kasar.

A jamhuriyyar Nijar kuwa, cutar tarin fukar na da kamari, saboda karancin kayyakin aiki da kuma gazawar hukumomi wajen bayar da abinci mai gina jiki ga masu fama da cutar.

A cewar Dr. Iliyasu Idi Mai nasara na kungiyar kwararrun likitoci na Nijar, ana bayar da maganin tarin fuka kyauta a fadin kasar.

Hakkin mallakar hoto spl

"Kuma idan mutum ya fara shan maganin daga kwana na farko har zuwa watanni shida bai yi fashi ba, to yana iya hulda da jama'a ba tare da ya sanya musu cutar ba." In ji likita.

Ya kara da cewa rashin kayan aiki ya sa idan mutane 100 sun kamu da cutar a kasar, ana iya warkar da kashi 75 zuwa 80 ne cikin dari.

Dr. Iliyasu ya kuma ce fiye da kashi goma cikin dari na masu fama da cutar na daina shan magani ko kuma ma ba a san inda suke ba.

Samun abinci mai gina jiki tare da shan magani ba fashi, na taimaka wa ainun wajen magance cutar tare da hana bazuwarta a tsakanin al'umma.