Sojojin Ukraine sun janye daga Crimea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun a yankin Crimea da ake fada a kai

Ukraine ta umarci sojojinta su janye daga Crimea bayan da Rasha ta kame sansanin sojinta na karshe dake tsibirin.

Shugaban riko na Ukraine Oleksandr Turchynov ya ce an dauki matakin ne saboda barazanar da Rasha ke yi wa rayuwar sojojin.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu, ya ziyarci Crimea domin duba sojoji da kuma kayayyakinsu a yankin.

Shi ne babban jami'in sojin Rasha da ya ziyarci Crimea tun bayan da Moscow ta shigar da yankin cikin kasarta.

A waje guda ma'aiktar tsaron Ukraine ta ce sun yi amfani da manyan makamai suka kwace wani sansanin sojin ruwa dake Feodosia a yankin Crimea.

Karin bayani