An fara shari'ar magoya bayan Morsi 682

Mohammed Badie Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun tarwatsa masu zanga-zangar goyen bayan Morsi lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 1000

Kotu a Masar ta fara shari'ar 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi 682, ciki har da Shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi, Mohammed Badie.

Sai dai Mr. Badie bai halarci zaman kotun ba, saboda abin da hukumomi suka kira dalilai na tsaro.

Shari'ar ta zo ne kwana daya bayan wata kotu a Masar, ta yanke wa wasu masu goyon bayan Mohammed Morsi 528, hukuncin kisa.

Amma wadanda ake zargin su 60 ne suka halarci zaman kotun, sauran ana yin shari'ar ne a bayan idonsu.

Badie da sauran mutanen za su fuskanci tuhuma game da tunzura mutane, su yi tashin hankali da kisan wasu masu boren adawa da kungiyar 'yan uwa Musulmi su takwas, a kofar shalkwatar kungiyar a Alkhahira.