An kashe mutane 15 a Bangui

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane na cikin firgici a Bangui

Kungiyar agaji ta duniya-Red Cross ta ce ta dauko gawarwakin mutane goma sha biyar da aka kashe tun ranar Asabar da ta wuce a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

An gano gawarwakin ne a wani yankin kasuwanci da aka fi sani da PK-5 a Bangui babban birnin kasar inda aka ruwaito dubban musulmi sun makale.

An sami barkewar arangama a yankin a karshen mako tsakanin Musulmi da mayakan sa kai Kiristoci da ake kira Anti-Balaka.

Shekara guda kenan tun bayan da 'yan tawaye suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Francois Bozize, lamarin da ya haifar da tarzoma da kuma kashe kashen ramuwar gayya tsakanin musulmi da kirista.

Karin bayani