Gawarwaki sun zo hannu a Jumhuriyar Afrika

Dakaru a Jumhuriyar Afrika ta Tsakiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakaru a Jumhuriyar Afrika ta Tsakiya

Kungiyar agaji ta duniya Red Cross ta ce ta sami damar dauko gawarwakin mutane goma sha biyar da aka kashe tun ranar Asabar da ta wuce a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

An gano gawarwakin ne a wani yankin kasuwanci da aka fi sani da PK-5 a Bangui babban birnin kasar inda aka ruwaito dubban musulmi sun makale.

An sami barkewar arangama a yankin a karshen mako tsakanin musulmi da mayakan sa kai Kiristoci da ake kira anti-Balaka.

Shekara guda kenan tun bayan da 'yan tawaye suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Francois Bozize lamarin da ya haifar da tarzoma da kashe-kashen ramuwar gayya tsakanin musulmi da kirista.

Karin bayani