'Yan sanda sun kwance bam a Kaduna

Image caption A shafe lokaci mai tsawo ba tare afkuwar tashin bam a Kaduna ba

Rundunar 'yan sandan jahar Kaduna a Nigeria ta kwance wani bam da wani mutum a kan babur ya jefa a wajen hada-hadar jama'a.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Aminu Lawal wanda ya tabbatar da hakan, ya jefa abun fashewa ne a cikin wata bakar leda a kan titi Sir Kashim dake tsakiyar birnin Kaduna.

A cewar kakakin jami'an 'yan sanda da aka tura wajen tuni suka kwance bam din.

Hakan na faruwa bayan da a 'yan kwanakin nan aka hallaka mutane fiye da dari a karamar hukumar Kaura, wanda hakan ya sa hukumomi suka tsaurara matakan tsaro a kudancin jahar.

A waje daya kuma sarakunan jahar ta Kaduna su na taro, da zummar ganin yadda zasu bullo wa matsalar tabarbarewar tsaro a jahar.

Karin bayani