Zargin yunkurin juyin mulki a Venezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Venezuela Nicolas Maduro

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya ce an kama wasu manyan Janar na mayakan sojin sama su uku, bisa samunsu da yunkurin tunzura yiwa gwamnatinsa bore.

Ba'a dai baiyana sunayen Janar Janar din ba.

Maduro ya fuskanci zanga zanga a kullum har kusan tsawon watanni biyu, bisa tsadar rayuwa da karuwar miyagun laifuka da kuma karancin kayan masarufi.

Mutane kimanin talatin ne suka rasu a zanga zangar daga bangarorin jam'iyyu.

A baya dai Maduro ya zargi bangarori masu ra'ayin rikau, wadanda ke samun goyon bayan Amurka, da haddasa tarzoma, a yunkurin shirya masa juyin mulki.