Mayakan Anti-Balaka abokan gaba ne - AU

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Faransa a Bangui

Shugaban rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya yace daga yanzu za su dauki kungiyar Kiristoci 'yan banga ta anti-balaka a matsayin abokan gaba.

Sanarwar da Jean-Marie Michel Mokoko ya fitar, ta biyo bayan fadan da aka yi kwanaki ana yi ne inda mutane kimanin ashirin suka rasa rayukansu.

'Yan anti-balakan suna ta kai harin ramuwar gayya a kan musulmi tun bayan da kungiyar 'yan tawaye musulmi ta Seleka ta kwace mulki shekara guda da ta wuce.

Janar Mokoko ya kuma zargi 'yan anti-balaka da kai hari a kan sojojin kiyaye zaman lafiya wadanda ke aiki tare da sojojin Faransa domin kwance damarar bangarorin biyu.

Karin bayani