An kashe mutane 60 a Benue

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An dade ana gaba tsakanin Tivi da Fulani

Rahotanni daga jihar Benue ta Nigeria na cewar an kashe akalla mutane sittin a cikin wasu hare-haren da aka kai wa wasu kauyuka na kabilar Tivi tsakanin ranar Litinin da Talata.

Wani mai magana da yawun gwamnatin jihar ya shaida wa BBC cewar hare-haren da ke da alaka da daddiyar gabar da ke tsakanin kabilar Tivi wadanda galibi manoma ne da kuma Fulani makiyaya sun afku ne a wasu kananan hukumomi biyu, inda ba a saba samun rikici ba.

Rikici tsakanin Fulani da Tivi ya janyu rasuwar mutane da dama a cikin 'yan watannin da suka wuce.

Ministan yada labarai a Nigeria, Labaran Maku a bangarensa, ya musanta zargin cewar gwamnatin tarayyar kasar ta gaza wajen shawo kan rikicin, inda ya ce dole ne sai gwamnatocin jihohi sun sa hannu.

Karin bayani