Rikicin Boko Haram ya rutsa da mutane miliyan uku

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria na sintiri a Maiduguri

Hukumar agajin gaggawa ta Nigeria-NEMA ta ce rikicin Boko Haram ya shafi akalla mutane miliyan uku a arewa maso gabashin kasar.

A cewar hukumar daga watan Junairu zuwa watan Maris na bana, mutane kusan dubu 250 ne suka rasa muhallansu a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Shugaban NEMA, Alhaji Muhammad Sani Sidi ya ce a jihar Borno lamarin ya rutsa da mutane fiye miliyan daya da dubu dari uku, a yayinda mutane fiye da miliyan daya musamman mata da kananan yara da kuma tsofaffi lamarin ya rutsa dasu a jihar Adamawa.

A cewarsa, a jihar Yobe inda aka kashe daliban kwaleji a Buni Yadi, rikicin ya rutsa da mutane fiye da dubu dari bakwai da saba'in.

Hukumar NEMA ta ce ta samu wadannan alkalumanne bayan wani aikin hadin gwiwa da ta gudanar tare da kungiyar agaji ta Red Cross da kuma kungiyoyin agaji na jihohin da abin ya shafa.

Binciken da hukumomin su ka gudanar kuma ya nuna cewar a yanzu haka dai galibin mutane a yankin arewa maso gabashin Nigeria ba sa iya cin abinci sau uku a rana.

Kungiyar Boko Haram wacce ta addabi yankin, dai ta kashe dubban mutane tara kona dukiyoyin al'umma.

A halin yanzu, jihohi uku a yankin arewa maso gabashin Nigeria na karkashin dokar ta-baci amma kuma hakan bai kawo karshen zubar da jinin da ake yi ba.

Karin bayani