Korea ta Arewa da makamanta

Shugaba Obama, da shugabar Korea ta kudu Park Geun-hye da Prime Ministan Japan Shinzo Abe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin suna tattaunawa ne kan barazanar makamai masu linzamin Korea ta Arewa.

Korea ta Arewa ta yi gwajin wasu makamai biyu da ake ganin makamai masu linzami ne da ake harbawa a jiragen ruwa.

Duk da cewa a baya Korea ta Arewar ta harba makamai masu linzami da dama da ke cin gajeren zango, sai dai wannan ne karon farko a shekaru biyar da ta harba makamai irin wanna.

An harba makamai masu linzamin ne sa'o'i kadan bayan da shugaba Obama ya gana da shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye da kuma Prime Misintan Japan Shinzo Abe a kasar Holland domin tattauna barazanar makaman Korea ta Arewa.

Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce gwajin makamai masu linzami da Korea ta Arewa ta yi kamar takalar fada ne da Amurkar ta damu da shi sosai.

Ta kuma kara da cewa Amurka na tattaunawa da kawayenta da kuma kwamitin tsaro na MDD dan maida martani, ta kuma bukaci Korea ta Arewa da ta kaucewa duk wasu matakai na barazana anan gaba.