CBN: Majalisa ta amince da nadin Emefiele

Image caption Ana bukatar goggagen masanin tattalin arziki don jagorantar babban bankin kasar

Majalisar Dattijan Nigeria ta amince da nadin Godwin Emefiele a matsayin sabon gwamnan babban bankin kasar.

Mr. Emefiele wanda shi ne Manajan Darektan Bankin Zenith zai soma aiki ne a watan Yuni, lokacin da wa'adin mulkin Malam Sanusi Lamido Sanusi wanda aka dakatar, ke karewa.

Haka kuma Majalisar Dattijan ta amince da nadin mai shari'a Zainab Adamu Bulkacuwa a matsayin shugabar kotun daukaka kara ta kasar.

Mai Shari'a Zainab Bulkacuwa wacce a hanzu haka take rikon kujerar, 'yar asalin jihar Gombe ce.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ne ya mika sunayensu ga majalisar dattijan kasar don ta amince kafin ya rantsar dasu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Karin bayani