Zartar da hukuncin kisa ya karu - Amnesty

Wani mutum da aka rataye a Iran Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amnesty ta ce akan kashe dubban mutane a kowace shekara

Kungiyar Kare Hakkin Bil adama ta Amnesty international ta ce, an samu karuwa sosai na hukuncin kisan da aka zartar a duniya a shekarar 2013.

Ta ce akalla mutane 369 ne aka zartar wa hukuncin kisa a Iran da kuma 169 a Iraki, abin da ya sa kassahen suka zama na biyu da na uku, a yawan zartar da hukuncin kisa.

Ban da alkaluman da hukomomi suka bayyana a Iran, Amnesty ta ce majiyoyi masu karfi sun ce an kashe wasu mutanen kimanin 369 a asirce.

Har yanzu China ce ke kan gaba wajen zartar da hukuncin kisa a duniya, ko da yake akan boye adadin.