An dakatar da neman jirgin Malaysia

Iyalan wadanda suka bata a cikin jirgin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fiye da 'yan asalin kasar China dari ne a cikin jirgin da ya yi batan dabo kusan makwanni uku.

Masu bincike na kasashen duniya a kudancin tekun India wadanda ke kokarin nemo jirgin Malaysian nan da ya bata, sun janye daga gudanar da aikin su na wucin gadi saboda rashin kyawun yanayi.

Ma'aikatan sun fuskanci matsananciyar iska da ruwan sama mai karfin gaske abinda wani jami'i ya kira da fidda tsammani.

Hukumomin Australia sun ce jiragen za su koma sansaninsu da ke birnin Perth na kasar, ya yin da aka bukaci jiragen ruwa da su janye daga wurin.

Masu aikin binciken dai sun maida hankali ne a wurare biyu da hotunan tauraron dan Adam da Frasansa ta gano na abubuwa fiye da dari da ashirin da suke kama da tarkacen jirgin.