Boko Haram:Kamaru ta cafke mutane uku

Image caption Dakarun Nigeria na sintiri a kan iyakokin kasar

Hukumomi a Kamaru sun ce sun damke wasu dulallan makamai su uku wadanda ake zargi suna da alaka da kungiyar Boko Haram a Nigeria.

Mutanen uku da aka tsare a lardin arewa mai nisa a ranar Laraba kusa da kan iyakar Kamaru da Nigeria, an kama su da manyan makamai da bindigogi kirar AK 47.

Rahotanni sun ce tuni aka garzaya da mutanen zuwa birnin Maroua inda jami'an tsaro ke musu tambayoyi.

Kungiyar Boko Haram wacce ta kaddamar da hare-hare a yankin Arewa maso gabashin Nigeria, ta kashe akalla mutane 1,000 a wannan shekarar, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar-NEMA ta bayyana.

A cikin watannin da suka gabata, gwamnatin Nigeria ta bukaci gwamnatocin kasashen dake makwabtaka da ita, su taimaka wajen murkushe ayyukan 'yan Boko Haram wadanda ake ganin cewar suna tsallakawa daga kasar su shiga cikin wasu makwabtan kasashe.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar tsaron Nigeria ta ce ta cafke wasu 'yan ta'adda a kan iyakoki kasar da Kamaru da kuma Chadi.

Karin bayani