Gwamnatin Nijeriya za ta sake shata burtali

Fulani makiyaya
Image caption Fulani makiyaya

A Najeriya, gwamnatin kasar ta bayyana cewa kimanin jihohi goma sha bakwai ne ke fama da rikicin Fulani da Manoma a arewaci da kuma kudancin kasar da ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

Kazalika gwamnatin na zargin cewa wasu mahara na rabewa da rikicin suna yin aika-aikarsu.

Yanzu dai Majalisar da ke kula da al'amuran tattalin arzikin Najeriyar ta yanke shawarar sake shata burtaloli da wuraren kiwo a kasar.

Sannan a bangare guda kuma jami'an tsaro sun dukufa wajen yaki da maharan.

Karin bayani