Kwankwaso ya soki taron kasa a Nigeria

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na Kano Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na Kano

Wasu gwamnoni a Nijeriya na ci gaba da sukar taron da ake gudanarwa yanzu haka, na lalubo hanyoyin warware matsalolin kasar.

Masu wannan ra'ayi dai na ganin taron zai kara kururuta matsalolin da Nijeriya ke fama da su ne maimakon warware su.

Wasu gwamnoni kamar na Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na ganin sabanin da ake samu tsakanin bangarori dabam dabam a wajen taron yana kara raba kan al'ummar Nijeriya ne.

Mahalarta taron dai sun samu gagarumin sabani tsakanin wasu bangarorin jama'ar kasar kan hanyar da za a bi domin amincewa da duk wani batu, abin da ya sa aka kafa wani kwamiti mai wakilai hamsin da zai lalubo hanyar waraware matsalar.

Gwamnan na Kano ya ya ce shi dama tun farko ba ya goyon bayan taron.

Karin bayani