Nigeria na son a maido da kudin Abacha

Image caption Margayi Janar Sani Abacha

Gwamnatin Nigeria ta bukaci a maido mata da dukiyar tsohon shugaban kasar, Janar Sani Abacha wacce gwamnatin Amurka ta kwace.

Kudi da kadarori na kusan dala miliyan 458 da ake zargin Marigayi Sani Abacha da mukarrabansa suka sace, a yanzu gwamnatin Nigeria take son a dawo mata da su.

Ministan Shari'ar Nigeria, Muhammed Bello Adoke shi ne ya bayyana matsayin gwamnatin kasar a wata sanarwa da ya fitar.

Tuni gwamnatin Amurka ta bayyana cewar ta kwacce kudade a asusun ajiyar kudi a kasashen duniya daban-daban mallakar Janar Abacha da kuma kaddarori wadanda ta ce ya mallaka ta hanyar da ba ta dace ba.

A cewar Minista Bello Adoke idan aka maido da kudaden za su yi amfani da su wajen yin abubuwan ci gaban al'umma.

Marigayi Janar Sani Abacha ya mulki Nigeria daga shekarar 1993 har zuwa karshen rasuwarsa a shekarar 1998.

Karin bayani