' Mun kashe tare da cafke 'yan ta'adda '

Sojin Najeriya na sintiri
Image caption Rundinar ta ce ta kashe 'yan ta'adda 7 tare da kama wasu karin da dama

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa a ci gaba da kakkauta sintiri a iyakokin Najeriya da Kamaru da Chadi ta sami nasarar cafke da kuma halaka wasu wadanda ake zargi yan taadda ne da dama.

Haka kuma a cikin sanarwar da ta fitar rundinar ta ce ta sami nasarar cafke wasu yan taadda,ciki har da wani sojin haya dan kasar Chadi da Burkina Faso, wanda kuma ke dauke da muggan makamai.

Rundunar ta ce a yanzu ta na kara kai farmaki a maboyar 'yan ta'adda a wadannan iyakoki na kewayen tafkin Chadi da suka hada da Kwatan, Kanwa, Kwatan Yobe da sauransu.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na rundinar sojan ta Najeriya.

Karin bayani