Yarjejeniyar zaman lafiya a Philippines

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An shafe shekara da shekaru ana yaki a kasar

Gwamnatin kasar Philippines ta sa hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da tarihi da kungiyar musulmi 'yan tawaye mafi girma a kasar.

Yarjejeniyar wani mataki ne na kokarin kawo kawo karshen yakin da yafi kowane dadewa kuma ya fi kowane muni a nahiyar Asiya.

An soma tattaunawa ne a hukumance tsakanin gwamnatin da kuma kungiyar Moro Islamic Liberation Front a shekara ta 2001.

Yarjejeniyar ta bai wa yankunan kudancin Mindanao da yawancin mazaunansu musulmi ne 'yancin cin gashin kansu inda su kuma za su daina tawaye da makamai.

Shugaban Philiphine din Benigno Aquino ya ce a baya can har shakku yake yi ta yiwuwar sasantawa tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai sauran kungiyoyin masu ta da kayar baya sun lashi takobin ci gaba da yakar gwamnati da sai an basu cikakken 'yancin kai.

Karin bayani