An zartar da doka kan 'yan luwadi a Sokoto

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gwamnatin Nigeria ma ta zartar da doka kan 'yan Luwadi

Majalisar dokokin jihar Sokoto a Nigeria ta zartar da wata doka da ta tsaurara hukunci a kan wadanda aka samu da laifin aikata luwadi da madigo da kuma fyade.

Majalisar ta ce, ta saurara hunkuncin ne musamman ta fuskar kudin tarar da wadanda suka aikata wadannan laifuka ke biya.

Wasu kungiyoyin kare hakkin mata a Nijeriya dai sun sha kokawa a kan cewa, kudin tarar da wadanda aka samu da aikata fyade ke biya bai taka kara ya karya ba, kuma hakan yana tsawwala matsalar.

Kakakin majalisar dokokin ta jihar Sokoto, Alhaji Lawal Muhammadu Zayyana ya bayyana cewar manufar sabuwar dokar ita ce don ganin an rage yawan masu aikata irin wadannan laifukan.

Karin bayani