An tarwatsa masu zanga-zanga a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Magoya bayan hambararren shugaban kasa, Muhammed Morsi

'Yan sanda a Masar sun harba hayaki mai sa hawaye a kan magoya bayan haramtacciyar kungiyar 'Yan Uwa Musulmi.

Kamfanin dillancin labaran gwamnati ya ce masu zanga-zanga wadanda suke ta rera wakoki sun yi dandazo a kudancin birnin, bayan sallar Juma'a amma nan da na 'yan sanda suka tarwatsa su.

An kara yawan jami'an tsaro a birnin Alkahira bayan da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta yi kiran magoya bayanta su gudanar da zanga-zanga dangane da kudirin Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi na tsayawa takarar shugabancin kasar.

Kasar ta Masar tana fuskantar tarzoma da tashe- tashen hankula tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi a bara.

Karin bayani