Al-Sisi: Masar ba ta sauya zani ba

Feild Marshal Abdul Fattah Al-Sisi

Kafin shekarar 2011 Misirawa ba su san mutumin dake shirin zama shugaban kasarsu ba, watau Feild Marshal Abdul Fattah Al-Sisi.

Hakan na nuni da kakagidan da sojoji ke yi a mulkin kasar da kuma dabarar karbe mulki na feild Marshal din a kashin kansa da wasu dalilai na rundunar sojin kasar.

Muhimmin abu game da iya siyasarsa shi ne sirri, bugu da kari kuma bakin ganga ne shi, ta yadda ya nuna wa abokan adawarsa cewa shi soja ne da bashi da dogon buri.

Yayin da a waje daya kuma ya nuna wa al'ummar Masar cewa shi ne mutumin da zai fitar da su, daga badakalar siyasar da ta auku bayan saukar Mubarak.

To ko wanene wannan jami'in wanda ba a san kansa ba? Kuma wadanne dalilai ne suka sa ta yiwu ya yi mulkin Masar.

Yaron Tantawi

Da farkon fari, Feild Marshal Sisi na cikin wani babban kwamandan soji, dake karkashin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.

Bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban mulkin sojin kasar Anwar Sadat, Mubarak ya dare karagar mulkin kasar, sannan ya zabi Mohammed Hussein Tantawi ya shugabanci kananan hafsoshi.

Mukamin dake nufin zai iya saka wa jami'ai masu biyayya da karin girma da basu goyon baya.

Field Marshal Sisi na daga cikin wadanda Feild Marshal Tantawi ke so, kuma yake baiwa ayyuka masu gwabi-gwabi.

An bai wa Sisi horon da ya kamata a kasashen waje, inda kuma ya kara goge wa ta hanyar yin karatu a Burtaniya da kwalejin sojoji na Amurka, haka kuma ya zama babban jami'in tsaro na ofishin jakadancin Masar a Riyadh.

Sannan an bashi jagoranci masu muhimmanci da suka hada da na bataliya da runduna da kwamnadan wani sashe, ya kuma zama hafsan soji.

Hakazalika ya rike mukami mai muhimmanci na mataimakin shugaban hukumar tattara bayanan sirri na kasar.

Daga wannan mukami ne, Tantawi ya dauko shi zuwa majalisar koli ta sojin kasar, wanda ta mulki kasar bayan an hambarar da Mubarak a shekarar 2011.

Aminci

Wata rayuwa ta al-Sisi mai muhimmanci ita ce, rawar da ya taka a bayan fage a matsayinsa na wakilin majlisar koli ta soji ga kungiyar 'yan uwa Musulmi, matsayin da Tantawi ba shi.

Ana daukar Sisi a matsayin mutum mai addini saboda irin ra'ayin rikau na gidansu, kana mutum ne mai yawan jan ayoyin kur'ani a maganganunsa, wadannan halayen ya sa kungiyar 'yan uwa musulmi ta amince da shi.

Hakan ya yi tasiri sosai, saboda shugaba Morsi ya zabo shi domin maye gurbin Tantawi, na babban hafsan hafsoshi da ministan tsaro na kasar, a watan Agustan 2012.

Sisi ya amince ya karbi mukamin bisa sharadin Morsi ba zai yi wa tsaffin sojoji bita-da-kulli ba, abin da ke nuna cewa ya samu mukami na kololuwa ba ta hanyar juyin mulki ga magabatansa ba, a'a sai ta hanyar kare su.

Yaudara

Shugaba Morsi da 'ya'yan kungiyar 'yan uwa musulmi sun yi amanna Sisi nasu ne, yayin da kuma ya ke tabbatar wa iyayen gidansa sojoji cewa yana kare ra'yoyinsu.

A bainar jama'a Sisi na jin kunyar Morsi, inda duk aka samu rashin fahimta a tsakaninsu, sai Sisi ya bada kai bori ya hau.

Image caption Gwamnatin Masar ta rikon kwarya mai samun goyon bayan sojoji ta haramta kungiyar 'yan uwa musulmi a Masar

Sai dai a game da batutuwan tsaro masu muhimmanci kamar yankin Sinai da mashigin Suez, Sisi ya yi farat ya riga shugaban kasar ta hanyar sanya doka, abin da ke nuna wa sojoji cewa ba zai lamunci sadaukar da batutuwa masu muhimmanci ga kungiyar ta 'yan uwa musulmi ba.

Ya zuwa karshe dai Morsi ya yi amanna cewa feild Marshal din na tare da shi, abin da ya sa ya yi watsi da sakon shi a ranar 1 ga watan Yuli, shekarar 2013 da ke cewa ko ya bi abin da mutane ke so, ko kuma soji su dauki mataki.

Kuma abin da Sisi ya fara yi bayan ya yiwa Morsi juyin mulki a ranar 3 ga watan Yuli, kuma ya tura shugaban kasar gidan kaso, shi ne sanya janar Mohammed Farid al-Tohamy a matsayin shugaban hukumar leken asiri na kasar.

Da umarnin Sisi Tohamy ya aiwatar da tarwatsa sansanonin masu zaman durshen, na magoya bayan 'yan uwa musulmi, abin da ya kai ga mutuwar mutane kimanin 1000.