Riga kafin Rotavirus a Kamaru

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin kasar na son rage yawan yara kanana da ke mutuwa.

A Jamhuriyar Kamaru, gwamnatin kasar na yunkurin cinma manufar sabon karni a fannin kiwon lafiya masamman ma wurin rage kason yara kanana masu mutuwa gabannin su cika shekaru biyar a duniya.

Akan haka ne ta kudurci shigowa da wani sabon alluran riga kafi da zai yaki kwayar cutar Rotavirus mai haddasa tsananin zawo ga yara kanana.

Riga kafin wanda za a fara a yau za'a yi shi ne ga kananan yara masu watanni goma sha daya da haihuwa izuwa kasa.

Wannan kuma zai zama allurar riga kafi na cikon goma sha daya (11) da hukumomin kiwon lafiya suka shigar cikin jerin riga kafin da ake yi wa yara kanana kyauta domin kada su kamu da wasu cutattaki.