Kira don kuri'ar raba gaddama a Ukraine

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Viktor Yanukovych

Hambararren Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych ya yi kira ga kowace gunduma a Ukraine ta gudanar da kuri'ar raba gardama a kan matsayinta a cikin kasar.

Da yake jawabi a Rasha, Mr Yanukovych ya ce daukar irin wannan mataki zai taimaka wajen daidaita Ukraine da kuma kare martabar 'yancinta na kasa.

Wannan dai shine kalaminsa na farko tun bayan da Crimea ta kada kuri'ar kasancewa cikin kasar Rasha.

Sai dai wani dan majalisar dokokin Ukraine Andriy Shevchenko ya shaidawa BBC cewa wadannan kalamai sun nuna cewa yunkurin Rasha na kutse a cikin kasar ba zai tsaya ga Crimea ba kadai .

Karin bayani