Kwamitin sulhu na taron kasa ya gama aikinsa

Wakilai a taron kasa
Image caption Wakilai a taron kasa

Kwamitin da aka dorawa alhakin warware takadamar da ta kunno kai game da tsarin da ya kamata a bi wajen amincewa da duk wani batu a babban taron kasa dake gudana a Abuja ya kamala aikinsa.

Kwamitin ya ce zai gabatarwa zauren taron matsayar da suka cimma ranar litini mai zuwa.

Malam Awalu Yadudu daya daga cikin mambobi hamsin da ke cikin kwamitin ya ce sun yanke shawara za su shaida ma taron ya aiwatar da yarjejeniya ta sulhu kuma ta fahimta da samun ra'ayi na mafi rinjayen jama'a a kan duk wata shawara da aka cimma.

Karin bayani