Putin da Obama sun tattauna kan Ukraine

Shugaba Putin da Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin biyu sun tattauna kan batun yiwuwar amfani da diplomasiyya akan rikicin Ukraine.

Shugabannin kasashen Amurka da Rasha sun tattauna yiwuwar amfani da mataki na diplomasiyya kan rikicin Ukraine.

Shugaba Obama da Vladimir Putin sun tattauna na tsahon sa'a a guda ta wayar tarho wadda shugaba Putin ne ya kirkire ta.

Fadar white House ta ce Obama ya bukaci a bada gamsasshiyar amsa kuma rubutacciya game da shawarwarin da Amurkar ta bada kan rikicin ukraine.

Obama ya kuma sake nanata lallai dakarun sojin Rasha su fice daga iyakar Ukraine.

Sannan shugabannin biyu sun amince ministocin kasashensu za su gana domin tattauna mataki na gaba.