Ana cigaba da neman jirgin Malaysia

Ana cigaba da neman jirgin Malaysia Hakkin mallakar hoto AP

Masu aikin neman jirgin Malaysia da ya bace sun kammala aikin yau ba tareda wani cigaba ba.

Jirage tara ne da kuma jiragen ruwa takwas suka yi aikin neman jirgin a tekun kudancin India.

Hukumomin Australia sunce abubuwanda aka gani a jiya kayan kama kifi ne da akayi dai na amfani dasu.

Wasu 'yan uwan wadanda ke jirgin da ake nema din sun isa Malaysia don neman bayanai daga hukumomin kasar akan bacewar jirgin

Karin bayani