An matsa kaimi a neman jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen dai sun hada da Australiya da Malaysia da China da Japan da New zealand da Amurka da kuma Koriya ta Kudu.

Kasashen duniya sun kara matsa kaimi waje neman jirgin Malaysian nan da ya bace, inda yanzu haka jiragen sama goma da na ruwa takwas ke aikin binciken a kudancin tekun India.

Wani jirgin ruwan Australia da ke iya gano na'urar nan ta black box da ke nadar bayanai cikin jirgin sama, ko da kuwa ta kai zurfin kilomita shida a cikin teku, ya shiga sahun masu binciken.

A ranar Asabar, an kwaso wasu tarkace daga cikin ruwan, amma babu wanda aka tabbatar daga cikin jirgin da ya bata su ke.

Kasashe bakwai ne suka tura wannan adadin na jirage domin binciken wanda ake yi a wani wuri mai tazarar kilomita dubu daya da dari takwas yamma ga gabar ruwan birnin Perth na yammacin Australia.

Karin bayani