Ana zaben kananan hukumomi a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr. Erdogan dai yayi yekuwar neman zabe sosai domin nema wa jam'iyyarsa goyon baya.

Al'ummar Turkiyya na jefa kuri'a a zaben kananan hukumomin kasar da ake yi yau Lahadi abinda ake gani a zaman wata dama gare su ta bayyana ra'ayinsu game da gwamnatin Firai minista Recep Tayyip Erdogan.

Wannan zaben dai shi ne na farko tun bayan da zanga-zangar da aka yi a watan Yunin bara da kuma bullar zargin tafka almundahana da ake yi wa gwamnatinsa.

Firai ministan dai ya kira masu adawa da shi maciya amanar kasa, inda ya bukaci magoya bayansa da su koya musu darasi.

Babbar jam'iyyar adawa ta CHP kuwa ta bayyana shi a matsayin maras gaskiya da ke mulkin kama-karya kuma mai fatan dore wa kan mulki ko ta halin kaka.

Karin bayani