Apple da Samsung sun koma kotu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Samsung ne kan gaba wajen sayar da wayoyin komai da ruwanka a duniya

Hamayyar dake tsakanin manyan kamfanoni biyu Apple da Samsung ya kara muni inda suka kara komawa gaban kuliya a California.

Apple na zargin Samsung da satar wasu daga cikin abubuwan dake tsarin wayoyinsa musamman ta yadda ake rufe wayar.

Amma Samsung ya ce shi ne ya soma wannan tsarin, kuma Apple ne ya yi satar.

Apple na son Samsung ya biyashi dala biliyan biyu saboda wannan zargin satar.

A karar da ya shigar, Apple ya ce shine ya fito sabbin tsare-tsare a wayoyin komai da ruwanka.

Sai dai Samsung ya mayar da martani game da wannan zargin.

A cewarsa, Apple ne tun farko ya yi satar wasu tsare-tsaren Samsung kuma shima yana bukatar diyya.

Samsung yace Apple ya kwaikwayi tsarinsa a iPhone da iPod da kuma iPad.

Karin bayani